1 Corinthians 13
1Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala’iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo. 2Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne. 3Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta,, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. ( Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya). 4Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai 5ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka. 6Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya. 7Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa. 8Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce. 9Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa. 10Sa’adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce. 11Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya. 12Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani. To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna. 13
Copyright information for
HauULB