‏ 2 Corinthians 3

1Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba? 2Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa. 3Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane.

4Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu. 5Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take. 6Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa.

7To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa. 8Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi?

9Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi! 10Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi. 11To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu!

12Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai. 13Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra’ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye.

14Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa’adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi. 15Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu. 16Amma sa’adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin.

17To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai ‘yanci. Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.

18

Copyright information for HauULB