3 John
1Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske. 2Ya kaunatace na, ina addu’a domin ka samu albarka cikin kowanne al’amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya. 3Na yi farin ciki kwarai sa’adda wadansu ‘yan’uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya. 4Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya. 5Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga ‘yan’uwa da baki, 6wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada, 7domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al’ummai. 8Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya. 9Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba. 10Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama’a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar ‘yan’uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya. 11Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba. 12Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce. 13Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba. 14Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa’annan mu yi magana ido da ido. 15Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.
Copyright information for
HauULB