‏ Acts 10

1An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya. 2Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu’a ko yaushe ga Allah.

3Wajen sa’a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala’kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala’ikan ya ce masa, ‘‘Karniliyas!‘’ 4Karniliyas ya zuba wa mala’ikan ido a tsorace ya ce ‘’Menene, mai gida?‘’ mala’ikan ya ce masa, ‘‘Addu’ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah, 5‘’Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. 6Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.

7Da mala’ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima. 8Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.

9Washe gari wajen sa’a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu’a. 10Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi. 11Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu. 12A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.

13Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci ‘’ 14Amma Bitrus ya ce ‘’Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba.” 15Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; “Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce.” 16Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.

17A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma’anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan, 18Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.

19A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.” 20Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su.” 21Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”

22Suka ce, “Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al’umman Yahudawa, shi ne wanda mala’ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka.” 23Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu ‘yan’uwa daga Yafa suka raka shi.

24Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci ‘yan’uwansa da kuma abokansa na kusa.

25Ya kasance sa’adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada. 26Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, “Tashi tsaye! Ni ma mutum ne.”

27A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya. 28Ya ce masu, “Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma’amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce. 29Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo.”

30Karniliyas ya ce “Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu’a da cikin sa’a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske. 31Ya ce, “Karniliyas, Allah ya ji addu’ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai. 32Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku. 33[Idan ya zo, zai yi magana da kai.]

34Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, “Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci. 35Maimakon haka, cikin kowace al’umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.

36Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra’ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka. 37Ku da kanku kun san al’amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi. 38Al’amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.

39Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace. 40Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne, 41ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,

42Ya umarce mu mu yi wa mutane wa’azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu. 43Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.`

44Sa’adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa’azin sa. 45Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al’ummai.

46Domin sun ji al’umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa, 47“Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?” Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.

48

Copyright information for HauULB