Acts 11
1Yanzu Manzani da ‘yan’uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al’ummai ma sun karbi maganar Allah 2Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi; 3suka ce, “Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!” 4Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce, 5Ina addu’a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana. 6Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama. 7Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.” 8Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.” 9Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.” 10Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama. 11Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni. 12Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan’uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin. 13Ya fada mana yadda ya ga mala’ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus. 14Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.” 15Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko. 16Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,”Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.” 17To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah? 18Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al’ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.” 19Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa’azin Yesu ga Yahudawa kadai. 20Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa’azin Ubangiji Yesu. 21Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji. 22Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya. 23Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su. 24Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji. 25Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu. 26Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista. 27A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya. 28Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko’ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya. 29Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa ‘yan’uwa da ke Yahudiya da taimako. Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu. 30
Copyright information for
HauULB