Acts 17
1Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami’ar Yahudawa a wurin. 2Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai. 3Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, ‘’Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu‘’. 4Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama’a da yawa. 5Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu ‘yan ta’adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama’a. 6Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu ‘yan’uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, ‘’Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana. 7Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.‘’ 8Da taron jama’a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu. 9Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran ‘yan’uwan, sai suka sake su. 10A wannan daren, ‘yan’uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami’ar Yahudawa. 11Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne. 12Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa. 13Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa’azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama’a. 14Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna. 15Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi. 16Sa’anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai. 17Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami’a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa. 18Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, ‘’Menene wannan sakaren ke cewa?‘’ Wadansu kuma sun ce, ‘’Da alama mai wa’azi ne na wasu alloli dabam,‘’ domin yana wa’azin Yesu da tashin sa daga matattu. 19Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, ‘’Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka? 20Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma’anar su.‘’ 21(Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su). 22Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, ‘’Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku. 23Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, ‘’Ga Allah wanda ba a sani ba.” Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku. 24Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu. 25Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu. 26Daga mutum daya ya hallici dukan al’umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa. 27Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu. 28A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, ‘Mu ‘ya’yansa ne’. 29Idan mu ‘ya’yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba. 30Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko’ina ya tuba. 31Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari’a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu‘’. 32Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba’a; amma wadansu kuma sun ce, ‘’Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar.‘’ 33Bayan haka, Bulus ya bar su. Amma wasu maza a cikinsu sun yarda da bisharar, sun ba da gaskiya, hade da Diyonisiyus dan Majalisar Tudun Arasa da wata mace mai suna Damaris, da wadansu tare da su. 34
Copyright information for
HauULB